(ABNA24.com) Kakakin ma’aikatar kiwon lafiya ta kasar Iran Kianoosh Jahanpoor ne ya sanar da cewa adadin mutanen da su ka warke daga kamuwa da cutar ta lumfashi “Covid-19” a fadin kasar ya kai 8,376.
Jahanpoor ya kuma ambaci cewa; Bayan da aka sake gano wasu mutane 1,411 da su ka kamu da cutar, yanzu jumillar adadin masu wannan cutar a fadin Iran ya kai 23,049.
Wani sashe na sanarwar ya kunshi cewa; ya zuwa yanzu an yi wa mutane miliyan 36 gwajin cutar ta Corona a dukkanin fadin kasar Iran, inda mutanen da shekarunsu su ka kai 50, su ka fi zama wadanda ke kamuwa da ita, yayin da masu shekaru 64 su ka fi zama wadanda ta ke kashewa.
A fadin duniya baki daya, adadin wadanda su ka kamu da cutar sun kai 343,000 yayin da wadanda su ka mutu kuma su ka kai 14,900.
A gefe daya, shugaban kasar Iran Dr. Hassan Rauhani ya kira yi ‘yan kasar da su rage yawan tafiye-tafiye a tsakanin gundumomi gwargwadon iko saboda a dakile yaduwar cutar.
Shugaban na kasar Iran ya kuma bayyana ana samun raguwar adadin wadanda su ke mutuwa da kuma kamuwa da cutar ta Corona.
/129
25 Maris 2020 - 06:36
Lambar labari: 1020264
Kakakin ma’aikatar kiwon lafiya ta kasar Iran Kianoosh Jahanpoor ne ya sanar da cewa adadin mutanen da su ka warke daga kamuwa da cutar ta lumfashi “Covid-19” a fadin kasar ya kai 8,376.